Question

Copied!

dan Allah ina tanbaya malam mai nene aki dar yan shi a kuwa

Asked by: Gaddafi assalafiy garo

Answer

Answered by: Dr. Muhammad Abubakar Adam

Alhamdulillah Wahdah, Wassalatu Wassalamu ala Rasulil-Lah, wa'ala Ālihi wasahbihi waman Wālāh. bayan haka. Amsa: Aƙidar yan shi'a itace a dunƙule kafirci da sunan Musulunci, shirka da sunan Musulunci, rusa Musulunci da sunan Kishin Musulunci da son ahlil baiti ( Iyalan Annabi) Yahudawa ne suka kirkiro ta domin yakan Musulunci da rusa shi daga cikin gida. Kaɗan daga cikin aqidan shi'a na kafirci sune: 1- Qudurce cewar Qur'ani bai cika ba, an canja shi, wai Sahabbai sun ciccire ababe acikin shi, sun saka wasu acikin shi, wanda wannan kafirci ne, ya sabawa abinda Allah ya faɗi a Alqur'ani na bashi kariya daga bata cikinshi har abada, haka ya sabawa amincin Sahabbai da Allah yafaɗi aqur'ani, haka ya sabawa dayawa daga hadisan Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam. 2- Qudurce cewa dukkan Sahabbai sun kafurta, sai kaɗai 'yan kaɗan waɗanda basu fi yatsun hannu ba. 3- Qudurce cewa Abubakar da Umar da Usman da A'isha da Hafsa da wasunsu duk kafirai ne, kuma Abubakar da Umar sune Gumaka kafirai ... 4- Zargin Uwar muminai A'isha R.A da zina, da da'awar zasu yi fito da ita daga ƙabari suyi mata duka... 5- Qudurce cewa imamansu sun sai gaibu, suna halittawa suna Kashewa suna rayawa da azurtawa... Wajibi akan kowa shine nisantar Addinin Shi'a da aqidunsu, da kasancewa akan aqidar salaf Assalih, Ahlissunah wajama'a, wacce take taqautuwa cikin kaɗaitawa Allah ibada da Tauhidi, da bin sunnar Annabinshi SAW, tare da yadda da dukkan Sahabbai da nema musu Yardar Allah, da kawar dakai akan dukkan abinda aka jingina musu da laifi ko aiki, da kuma koyi da su, kaman yadda Allah yai umurni da haka acikin Alqur'ani gurare da yawa, haka Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama yayi umurni da hakan acikin hadisanshi ingantattu. Wasallahu Wasallama ala nabiyyina Muhammadin wa'alihi wasahbihi ajma'een.

Answered on May 16, 2026

Answered

Related Fatwa

Mallam Ni mutum ne me yawan aikata istiminai,pls abani shawara

kaji tsoron Allah ka kuma guji duk abinda zai kai ka zuwa ga aikata wannan laifin kaman kallon video ko hotuna da basu dace ba. sai kuma ka yawaita a...

Read Full Answer →

menene hukuncin auren matan da tabar mijinta tsawon shekara bakwai ba da izininsa ba?

Alhamdulillah Wahdah, Wassalatu Wassalamu ala Rasulil-Lah, wa'ala Ālihi wasahbihi waman Wālāh. bayan haka. Amsa: Wacce tabar gidan mijinta koda na...

Read Full Answer →

Assalamu alaikum warahmatullah malam Dan Allah ya halarta mace tayi sallah da niqaf a fuskarta

Wa'alaikussalamu Warahmatullah Wabarakatuh. Amsa: Ya halatta tayi hakan, musamman idan akwai namiji wanda ba Muharraminta ba a gurin. Allah yai ma...

Read Full Answer →

Assalamu Alaikum warahmatullahi wabaraka (Kalmar Bari بارى) tana cikin sunayen Allah? Idan za'akora...

Wa'alaikussalamu Warahmatullah Wabarakatuh. Amsa: Eh, hakane, Abdul-Bari za'a ke kiran shi, kamar dai sauran Masu sunayen irin hakan; Abdullah, Abdu...

Read Full Answer →

Aslm malam. Don Allah ya ake hudubar sawa yaro suna? nagode

Wa'alaikussalamu Warahmatullah Wabarakatuh. Amsa: Babu Wata huduba da aka shar'anta domin sanya wa yaro suna a musulunci. wajibi shine zaba mai suna...

Read Full Answer →

malan ni mutum ne me yawan kokanto da raye raye na zuciya haka yasa kome nayi senaringajin riya n...

Sai ka din ga addu,ah Allah ya yaye maka

Read Full Answer →