Fatwa

Islamic legal opinions and answers to your questions

As salamu Alaikum Malam ina da tambaya. Aiki ne ya kaini daga. kano state zuwa Edo state. dan Allah mlm na tsawan kwana nawa ne zan iya yin sallah kasaru.

Copied!
Answered by: Ustadh Auwal Abdullahi Usman • Sep 18, 2026 Answered

Wa alaikum slm, Wasu malamai suna ganin cewa daga kwana uku shike nan, wasu kuma suna ganin sai ka dawo. Wallahu Ta'ala A'alam

mace data yi barin ciki wata Daya,shin zata daina sallah?

Copied!
Answered by: Ustadh Auwal Abdullahi Usman • Sep 15, 2026 Answered

Zata iya yi, be kai ace an hura masa rai ba, sabo da haka ba jinin haihuwa bane,

assalamu alaikum Mallam shin ko yahalatta mutum yayi sallah yayi karatun alqur,Ani da azumi domin nemama mahaifiyata Lada idan koma Bai halatta ba Yaya kamata inyi domin nemama Lada da ko gafara nagode Mallam Allah ya sakamako da alheri

Copied!
Answered by: Ustadh Auwal Abdullahi Usman • Sep 15, 2026 Answered

Wa alaikum slm, ya halatta kayi duk wani aikin alkhairi kayi tawassuli dashi kayi addu'a wa iyayen ka. zaka iya yin sadaka da niyyar Allah ya kai musu ladan

Assalamualaikum malam barka da dare Dan Allah tambaya ta a nan idan naxo masallaci na samu raka'a biyu na magrib ban samu dayan ba bayan an gama sallah na tashi na Idah sallah sai wani yaxo ya bi sallah ta shin ya halatta ko koma bai hallata ba.

Copied!
Answered by: Ustadh Auwal Abdullahi Usman • Sep 15, 2026 Answered

Wa alaikum slm, ya halatta ya bika shima ya samu ladan jam'i

aslm mlm dan Allah menene hukuncin Wanda y Daura laya

Copied!
Answered by: Ustadh Auwal Abdullahi Usman • Sep 15, 2026 Answered

Wa alaikum slm, ya aikata mummunan laifi da zai iya kaishi ga shirka

assalamualaikum mlm stakanin yin salatin annabi da istigfari wanne yafi falala

Copied!
Answered by: Ustadh Auwal Abdullahi Usman • Sep 10, 2026 Answered

Wa alaikum slm, ko wanne yana da falala kuma ko wanne ana buƙatar musulmi yayi. Salatin Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama duk wanda yayi ɗaya Allah zai yi masa goma, ana so kafin mutum yayi addu'a ya karanta. Istigfari neman gafara ne a wajen Allah, sannan in mutum yana yi sai samu biyan buƙata duniya da lahira.

As salamu Alaikum mln dan Allah ina da tambaya. Me nene mafi yawan kwanakin yin sallah kasaru

Copied!
Answered by: Ustadh Auwal Abdullahi Usman • Sep 01, 2026 Answered

Wa alaikum slm, akwai saɓanin malamai akan wannan mas'alar, wasu suna ganin cewa daga kwana uku za'a bar yin ƙasaru, wasu kuma sun ce ba adadi har sai mutum ya dawo.

As salamu Alaikum Malam ina da tambaya. Mene halaccin yin A,uziyya da Bismillah idan zeyi ikama.

Copied!
Answered by: Ustadh Auwal Abdullahi Usman • Sep 01, 2026 Answered

Be halatta ba

assalamu alaikum Mallam nine mahaifiyata Allah yayimata rassuwa sai yakasance danida babana kawai ke gadonta kasan cewar bani da yannai ko kannai sai babana yace ya yafemin nashi rabon Amma Yana da wasu ya'yan daban shin ko yahalatta??? nagode Mallam Allah ya sakamaka da alheri

Copied!
Answered by: Ustadh Auwal Abdullahi Usman • Sep 01, 2026 Answered

Wa alaikum slm, idan sauran ƴaƴan ba mahaifiyar ku ɗaya bane dama basu da gadon ta. Ya halatta ya yafe maka rabon sa idan ku biyu kawai zaku ci gadon ta. Koda akwai sauran magadan, idan aka raba zai iya yafe maka

Assalamu alaikum wa rahmatullah Wa barakatuh Malam tambaya ta anan shine menene hukuncin sallah kasaru a kan tafiya shin an kiyasta adadin kwanaki a shari'a wanda idan mutum yayi kasan ya sauka ta kanshi?

Copied!
Answered by: Ustadh Auwal Abdullahi Usman • Sep 01, 2026 Answered

Wa alaikum slm, akwai saɓanin malamai akan wannan mas'alar, wasu suna ganin ba iyakar kwanaki, wasu kuma kaman Mazhabar Malikiyya suna ganin cewa iya kwana uku ne kawai za'a yi ana ƙasaru.

Assalamu Alaikum warahmatullahi wabaraka tuh ya sheakh idan akahade sallah magariba da isha'i shin mutun Yana iyayin nafila ko bari zaiyi sai lokacin Isha yayi sannan yayi nafilar Allahu a'alam

Copied!
Answered by: Ustadh Auwal Abdullahi Usman • Sep 01, 2026 Answered

Wa alaikum slm warahmatullah, zaka baki sai lokacin Isha yayi kayi Witri

Assalam Alaikum. Don Allah Me Ne Hukuncin Sana'ar (Kwalliya) Ta Mata Ko Kuma (Make Up) A Musulinci? Allah Ƙarawa Malam Lafiya Da Imani.

Copied!
Answered by: Ustadh Auwal Abdullahi Usman • Sep 01, 2026 Answered

Wa alaikum slm, ya halatta matukar an kiyaye abinda Shari'a ta iyakance. idan mace ce zatayi wa ƴan uwanta mata kuma ba cakuduwan maza da mata a wajen, ba laifi